Mai magana da yawun Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya ce har kawo yanzu “babu sisin da ya zo hannunmu” na biliyoyin nairorin da attajiran kasar da bankuna da kamfanoni suka ambata bayarwa a matsayin gudunmowar yaki da cutar korona.

Attajirai irin su Aliko Dangote da Femi Otedola da Abdulsamad Rabiu da Herbert Wigwe da kuma Segun Agbaje sun bayar da gudunmawa mai tsoka don kawar da cutar a kasar.

Haka kuma hukumomi daban-daban su ma sun sanar da bayar da tasu gudunmawar, na baya-bayan nan ita ce gudunmawa daga tarayyar Turayyar turai inda ta sanar da bai wa Najeriya tallafin kudi euro miliyan hamsin don yaki da cutar korona.

To sai dai mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya ce “duk wadannan kudade na alheri da manyan ‘yan kasuwa da bankuna da masana’antu ke bayarwa, sisin kobo bai zo hannunmu ba, a kayan aiki da aka bayar sun karba sun aiki da su.”

Dangane da kudin da Tarayyar Turai ta ce za ta bai wa Najeriya kuwa, Malam Garba ya ce “Kudi ne da za su biya cikin wani asusu da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa don Najeriya saboda haka ba kaitsaye za su miko wadannan kudade ba.

Wannan asusu da aka kafa can kungiyar Turai za su saka wannan kudi euro miliyan 50, kudi ne da suka ware don gudunmawa ga kasashe daban-daban a ciki kuma suka ce Najeriya an ware mata miliyan hamsin na euro.”

Daga karshe Garba Shehu ya ce sai an zauna an kididdige wadannan abubuwa, “amma dai ba na zaton kudi ne za a dauka wuri na gugar wuri su miko shi ga Najeriya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *