CORONA VIRUS: Shugaban Kungiyar Izala Reshen Garin Zariya Malam Sani Yakubu, Mutumne Mai Biyayya Ga Umarnin Gwamnati, Babu Wani Limami Daya Cire Daga Kan Kujerarsa – Dan Saboda Kawai Limamin Yayi Biyyaya Ga Dokar Da Gwamnatin Jiha Ta Kafa, A Yunkurinta Na Dakile Yaduwar Annobar Cutar Sarqe Numfashi Ta (COVID 19) A Fadin Jihar.

— Inji Mazauna Unguwar Gayen Lowcost Dake Garin Zariya.

Shugaban kungiyar jama’atul izalatul bidi’a wa’iiqamatus sunnah (JIBWIS) reshen garin zariya, Malam Sani Yakubu bai cire limamin masallachin khamsu – salawat na Shiek Abubakar Gumi gayen Lowcost dake a cikin garin zariya ba, Asshiekh Malam Abubakar Sarki Aminu, kamar yadda ake rade-radin cewa wai dan saboda shi Shiekh Malam Abubakar din yayi biyyaya ga dokar da gwamnatin jiha ta kafa akan masallatai da majami’u da sauran guraren da suke haddasa cinkoson al’umma a fadin jihar, duk a yunkurin gwamnatin jihar na ganin ta dakile yaduwar wannan cuta ta (COVID 19), a tsakan -kanin al’umma.

“Hakika babu qamshin gaskiya acikin wannan labarin da ake yadawa a wasu daga cikin kafofin watsa labarai na yanar gizo, da kuma shafukan sada zumunta na zamani, sam wannan batu ba haka yakeba, hasalima an cireshi ne sakamakon yawaitar korafe-korafen da al’umma sukeyi akansa, abisa zarginsa da rarraba kawunan al’umma massalata da yake yawan yi, tare da siyasantar da sha’anin gudanar da masallachi wajen ibadar ALLAH (SWT), tare da qin yin biyyaya ga tsarin shuganbanchin Kungiyar Jama’atul – Izalatul- Bidi’a Wa’iiqamatus Sunnah Reshen Garin Zariya.”

“A karshe bayan cireshi da akayi a sakamakon wadannan dalilai, shugabanchin kungiyar izala na jihar Kaduna, reshen garin zariya ya amince da nada Asshiekh Malam Alhaji Tijjani a matsayin sabon limamin da zai jagoranchi wannan massallachi, tare da bada dukkan wani hadin kai da cikkaken goyan baya dari bisa dari, kan duk wani yunkuri da gwamnati xatayi wajen ganin an kawo karshen wannan cuta data addabi al’umma….”

Daga – Masu Rajin Kishin Al’ummar Kofar Gayan Lowcost, Zariya Dake Jihar Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *