Masu bibiyar kafafan sada zumunta na ganin cewa kwamishinan ayyuka na jihar Kano Mu’azu Magaji Dan Sarauniya ya rikide ya koma dan social media.

Hakan dai ya biyo bayan yadda kwamishinan ke kara matsa kaimi wajen wallafa ra’ayoyin sa ba dare ba rana a shafin sa na Facebook.

Sai dai da alama ra’ayoyin nasa basa yiwa wasu dadi, musamman tsagin masu adawa da kuma bangaren masoyan Sarkin Kano Mai Murabus Malam Muhammadu Sanusi II.

Sai dai bangaren magoya bayan jam’iyya mai mulki ta APC suna nuna goyon bayansu kan irin yadda kwamishinan ke kan gaba cikin masu baiwa jam’iyyar kariya a dandalin sada zumunta na Facebook.

Kwamishinan ya wallafa kalamai da dama musamman kan dambarwar tsige Sarki Sanusi II da gwamnatin Kano tayi.

Amma ya samu martani da dama daga dimbin al’umma, inda wasu ke ganin cewa bai kamata ga kwamishina guda ya rika biyewa dambarwar kafafan sada zumunta ba.

Ciki kuwa har da fitaccen Dan jaridar nan Ja’afar Ja’afar wanda yayi tsokaci kadan,  wanda ya nuna rashin jin dadin sa kan yadda kwamishinan yake gudanar da al’amuran sa a Facebook, sannan ya bashi shawara a irin salon nan na gyara kayanka.

Tsagin magoya bayan jam’iyya mai mulki kuwa na nuna goyon bayansu kwarai ga Kwamishinan ganin yadda ke kan gaba cikin jerin masu tallata muradan gwamnatin Kano da kuma bata kariya ta shafin na Facebook.

Tsokacin Ja’afar Ja’afar bai yiwa kwamishinan dadi ba, domin kuwa yayi martani ga Ja’afar din, ya nuna cewa yana nan akan bakansa na cigaba da wallafa ra’ayoyin sa.

Yanzu haka dai jama’a da dama na cigaba da yin tsokaci kan wannan batu inda kowa ke ta bayyana mabanbantan ra’ayoyi akai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *