Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bayyana sunan Federico Valverde a matsayin jigon nasararta ta dage kofin Spanish Super Cup yayin wasan da ya gudana a birnin Jidda na Saudiya, dai dai lokacin da magoya bayan kungiyar ta Real Madrid ke ganin kamata ya yi Club din ya yi mutum-mutuminsa saboda kasadar da ya dauka da ta kaisu ga nasara.

Yayin wasan dai wanda aka bai wa Valverde lambar zakaran wasa wato ‘‘man of the match’’duk kuwa da jan katin da ya samu da ya kaishi ga karkare wasan a wajen fili, an ga yadda dan wasan mai shekaru 21 ya tade kafar Alvaro Morata na Atletico Madrid lokacin da ya ke gab da zura kwallo a ragar ta Real Madrid, amma duk da hakan Club din ya bayyana shi a matsayin wanda ya cecesu.

Masu sharhi kan wasanni dai sun kwatanta kasadar ta Federico Valverde da irin wadda Lius Suarez yayi a gasar cin kofin duniya 2010, lokacin da ya sanya hannu ya tare kwallon da Ghana ke shirin zurawa a ragar Uruguay cikin a minti na karshe na tashi daga wasa wanda daga shi ne za ta iya yin waje ko kuma ta doke Uruguay kai tsaye a zagayen gab da na kusa dana karshe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *