Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar ganduje ya nemi hadin kan dukkanin al’ummar jihar Kano akan suzo a hada kai domin samarwa Kano ci gaba mai dorewa biyo bayan Nasarar da ya samu a kotun daukaka kara a jiya litinin.

Jim kadan bayan bayyana shi a matsayin halastaccen gwamnan Kano, gwamnan ya nemi dukkanin yan adawa da su ajiye makaman su, ta yanda za’aciyar da Kano gaba.

A cikin bayanin ya ambato sunan tsohon mai gidan sa Sanata Dr Rabiu Musa Kwankwaso da tattausar murya, bayan ya bayyana cewa ya yafe masa dukkanin abun da yayi masa sakamakon siyasa sannan ya nemi da yazo ayi tafiya tare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *