Wata musiba da ta riga ta zama ruwan dare a yankin Niamey dake jamhuriyar Nijer shine yanda ‘yammata, zawarawa wani lokacin ma har da matan aure kan yaudari samari su kaisu boyayyen waje sannan suyi musu fyade ta qarfin tsiya.

Wakilin Jaridar Tsanya ya tattauna da daya daga cikin wani Matashi da wannan iftila’i ya rutsa dashi, ya bayar da labari kamar haka;

“Wata kyakkyawar Budurwa tazo ta yaudareni da irin yaudarar su ta mata, suka kaini wani wajan cin abinci(restaurant), bayan mun gama ci sai tace na rakata gidan su, zuwan mu ke da wuya sai ta fara shafamin jikina nima ina shafa nata, jikina ya fara nauyi kenan sai naji an rufo kofar gidan; ashe ta hada baki da wasu qawayenta su biyu, nan take suka shigo suka rufar min har sai da na galabaita, bayan sun gama wahalar dani ne kuma suka daukeni suka jefar dani akan hanya”

Sai dai bayan da wakilin namu ke tambayar wannan matashi akan cewa anya kuwa Gardi kamar shi ace wai mata sunyi masa fyade? Sai yace; ” Gaskiya da farko ba tursashi sukayi ba, da sanin sa ya bisu, to sai dai daga baya ne bayan sun tarar masa abun yafi qarfin sa.

Yayin da wakilin namu ke tattaunawa da wata mata wacce tace tasan wasu daga cikin yammatan dake aikata wannan lamari; amma sukanyi amfani da Magani ne bayan sun yaudari namiji sun kaishi inda zasu aikata wannan lamari, daga baya idan suka gama biyawa kansu buqata a lokacin sun riga sun gama galabaitar dashi ne zasu dakko shi su jefar dashi akan hanya a mace ko a raye babu ruwan su.

A ta bakin wani Mazaunin Kasar ta Niamey ya bayyana cewa tabbas akwai wadannan mata, amma sukan samu Nasara ne akan kwadayayyun Samari da kuma irin ‘yan bana-bakwai masu biye-biyen yammata.

Wannan lamari ya zama ruwan dare a yankin na Niamey kamar yanda wata Mata da ta buqaci a boye sunanta ta bayyanawa wakilin namu.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *