Wata likita mai hada maganin gargajiya Dr Ebenezar ta yi kira ga maza da su rika saduwa da matansu akalla sau 21 a duk wata ko kuma sau biyar a kowane mako.

Likitar ta ce yin hakan na bayar da kariya ga maza daga kamuwa da cutar dajin dake kama ‘ya’yan maraina.

Bisa ga rahoton binciken da suka yi akan maza 32,000 ya nuna cewa mazan dake yawan saduwa da matan su basu kamuwa da cutar dajin dake kama ‘ya’yan maraina.

Ebenezar dake da asibitin gargajiya mai suna ‘Amuzu Hospital’ a jihar Imo ta ce ta yi wannan kira ne bisa ga sakamakon binciken da likitoci daga jami’ar ‘Havard’ dake kasar Amurka suka yi kuma aka wallafa a jaridar kasar.

Wani jami’in kungiyar likitocin kasar Amurka Dr James Balch ya tabbatar da haka inda ya kara cewa namiji zai iya samun wannan kariya ne idan ya hada da jima’I da cin abincin da zai kara masa karfin garkuwar jiki.

Bayanai sun nuna cewa cin ‘ya’yan itatuwa, ganyen da ake ci, dabino, madara,aya, namijin goro da dai sauran su na kara wa maza kuzari.

Idan ba a manta ba a watan Fabrairun 2019 ne likitoci suka bayyana cewa maza bakaken fata musamman ‘yan kasashen Afrika sun fi kamuwa da wannan cuta.

Bincike ya nuna cewa wannan cuta na daya daga cikin cututtukan dake yawan kisan maza a duniya.

Alamun wannan cuta sun hada da rashin iya yin fitsari yadda ya kamata,yin fitsari da jini,ciwon kirji da sauran su.

Likitoci sun bayyana cewa shan taba,shan giya na kawo cutar sannan akan iya gadon cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *