Kamar yadda kowa ya sani a zamanin nan bu wani abu da zaka yiwa al’umma a matsayin ka na mai mulki ko attajiri ko wani hamshakin dan kasuwa ka taimake ta irin ka bata ilimi domin da shi ne kowace al’umma take ci gaba a fannonin rayuwa, kamar yadda aka samu wani mai kishin mutanan sa a jihar Kano wato shugaban ƙaramar hukumar Gwale mai suna Hon. Dakta Khalid Ishak Ishak Ɗiso ya haɓaka tare da kawo ci gaba a hakar ilimin a yankin da yake wakilta wanda suke da gundumomi goma kuma ya yi wannan aikin a cikin shekaru biyu da ya yi a kujerar mulkin sa.

Mataimaki na musamman ga shugaban ƙaramar hukumar Gwale a fannin kafofin sadarwa Mallam Anas Saminu Ja’en ya ce a ziyarar da aka yi da kewan duba aiki da aka yi an zagaya makarantu kusan kimanin 40 wanda aka yiwa masu gyare-gyare a wasu makarantun da ginin sabunta ajujuwa da zuba kujerun zaman ɗalibai da gyara banɗakuna da samar da ruwan sha da samar mai tsafta samar da kayan koyo da koyarwa wanda zai sa ɗalibai jin daɗi. Kuma ya samar da wurin yin ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa ga malamai da ɗaliban su domin tafiya da zamani.

Haka a abun yake a wajan samawa ɗaliban ƙwararrun malamai wanda suka karanci fannin koyo da koyarwa, kuma makarantun da aka gyara da sabun tasu da zuba musu kayan da duk ake buƙata na harkar ilimi musamman ɓangaren gine-gine akwai makarantar Abdullahi Abbas Junior Model Secondary School da Sabere Firamare da Firamare dake Goron Dutse mai suna Hon. Khalid Ishak Ɗiso da wata a bayan ITF dake Ɗorayi da wata a Tunga da Unguwar Wambai da Rinji Firamare da (Girl Child Education) a Warure sauran sune Dandago Firamare da Sudawa Firamare da Ƙofar Waika Firamare da Muhammad Maigadon Kaya Firamare da Makarantar A.K kuma shi ne shugaban ƙaramar hukumar da a jihar Kano ba shi dana biyu domin da hawa da ya nemo wurare da aka gidana Firamare sama da 15.

Bayan wannan duk a ƙarƙashin sa kimanin yara maza da mata 12,133 ne suka yi jarrabawar Common Entrance a shekarar 2018/2019 wanda dukkannin su yanzu haka suna makarantun gaba da Firamare, kuma akwai yara 6 da suka tafi Unity School da samarwa yara maza da mata kayan makaranta har kimanin guda dubu ashirin da daya 21,000 da samawa yara 6 makaranta a janhuriyar Nijar kuma yara sun rabauta da kayan aiki a makarantu 364 akwai tsari tallafawa Islamiyoyi da Limamai wanda shugaban ƙaramar hukumar Gwale ya sahale duk bayan wani lokaci a ringa tura su bita domin ƙaro ilimi a fannin su kuma wannan aiki ɗan tsakuro shi kurum aka yi.

A zantawarmu da shugaban ƙaramar hukumar Dakta Khalid ya ce a irin wannan rayuwar da ake ciki babban abun jin daɗi da zaka yiwa kowace irin al’umma shi ne ka bata ilimi ingantacce, shi yasa na zaɓi na taimaki yara ta kuma ina alfahari da ilimi a koda yaushe domin shi ne ya kawoni wannan matsayi kuma ina fatan bayan tafiya ta ma wani ya ɗora. Babban abun da nake son har kullum shi ne naga harkar ilimi ta ci gaba a Gwale dama jihar Kano kuma sai Allah ya haɗa mu da abokan aikin masu ƙwazo suma suka bani haɗin kai sannan mun samu jajirtaccen gwamna mai kishin ilimi ko a dawowar da ya yi a wannan mulkin karo na biyu kuna ganin inda ya ƙaddamar da sabon tsarin ilimi kyauta kuma dole a faɗin jihar Kano, bayan nan akwai tsare-tsare da dama da zamu yi nan gaba a fannin lafiya da sauran ɓangarori da a hanyoyin da za a taimaki rayuwa ɗan adam musamman yaran mu da suke tasowa suma mu saka musu ƙarƙashin abun tun suna yara bayan sun girma suma sai su taimaki na ƙasa da su.

Kuma da shigowar shugaban ƙaramar hukumar Gwale mai girma Chairman Khalid Ishak Ɗiso ya dauki matakin gaggawa gyaran ilimi, a lokacin sa ne wadannan makarantu suka samu tagomashi kamar makarantar Filin Tsamiya Firamare da Ƙ/Waika da makarantar ƴaƴan Fulani ta Bajallabe da Firamare ta Ƙ/Kabuga da ta Maigadon Kaya da makarantar Annaja Islamiyya dake Sanimainagge da Firamaren Sanimainagge sauran su ne makarantar Firamaren Gwale SPS da makarantar K/Na’isa da makarantar Ta’alimul adfal Islamiyya Magashi da makarantar Yar Karofi Community School da wata makarantar Sabon Sara Community da Khadija Islamiyya Kabuga tare da makarantar Ahliyya Islamiyya, Darul Ma’arif da Nana Aisha Islamiyya duk a Warure da Gyaranya Islamiyya Nurul Haqqi Islamiyya Sudawa da makarantar Ma’ahad da Irshadu-Subyan da suke Dandago akwai ragowar wurare da dama da suka amfana da gyara tare da sabunta gine-ginen makarantun na su kamar makarantar Ɗorayi Babba SPS da makarantar Nasharul Ulum Islamiyya Ɗorayi U/Bello da Tahir Islamiyya da makarantar Ja’en Firamare da makarantar Shamsuddin Islamiyya Firamare, Ashabul-Kahfi Islamiyya duk a Sabon Gida da makarantar Abdurrahman bn Auf Islamiyya da makarantar Ta’alimuddeen Islamiyya dake Sanimainagge da sauran su da daman gaske da suka amfana bisa jajircewar – Dakta Khalid Ishak Ɗiso.

Masu karatu ku duba wannan abubuwa da aka yi domin ciyar da harkar ilimi gaba aikin shugaban ƙaramar hukumar Gwale wanda alamu sun nuna ba shi da na biyu a cikin tsakwarorin sa, shi ba gwamna ba shi ba ɗan majalissar jiha ko tarayya ko Sanata ba amma ku duba abun da yake ya yiwa ilimi a cikin shekaru biyu kacal. Kuma suna da yawan makarantu kusan kimanin 330 karamar Sakandire ta kai guda 63 kuma yawan adadin yaran maza da mata da suke da su a makarantu sun kai 126,583 suna da Malamai maza da mata har guda 2,875 duk watan duniya shugaban ƙaramar hukumar yana biyan albashi Malamai Naira 160,541,814.90 wanda su kuma Malaman jihar dake Gwale ake biyan su Naira 21,406,023.49 kuma jimillar kudin suka kama Naira 181,947,838.39 da ake bawa Malamai duk watan duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *