A daidai lokacin da ya rage saura kwanaki goma sha bakwai 17 a rantsar da sababbin gwamnatoci na tarayya dana jihohi..

Gwamnan zamfara mai barin gado Abdul’aziz Yari yai wani furuci game da batun mika mulki a ranar 29 ga watan Mayun nan da muke ciki, inda yake cewa : SSG Zai mika gwamnati ga duk wanda doka ta ce aba ranar Mika mulki, ni zan je ibadar Umrah, inji AS Yari.

Lamarin zaben jahar zamfara dai abune dake da cuku-murda ciki duba da hukunce-hukunce mabambanta da wasu ko tuna sukai kan batun zaben fidda-gwani na cikin jam’iyyar APC mai mulkin jahar.

Ya kuke kallon wannan furuci na Gwamna AA yari?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *