Wannanfa shine wai gaba da gabanta a wannan wata mai alfarma da muke ciki na Ramadana jaruma Maryam Yahaya ta halarci kasar Saudia domin gabatar da ibadar Umara, sai dai a wani salo na ban dariya Jarumar wadda ke jan zare acikin jerin jaruman dake da yawan masoya taci karo da fitaccen gwarzon dan wasan kwallon kafar nan Pogba a kasar ta Saudia.

Ganin Pogba ke da wuya sai ga Marya ta rikice cikin shauki da farin ciki na murnar haduwa dashi inda ta dinga kiran “Laaa! ga Pogba, Wallahi ga Pogba” wannan batu dai ya jawo cece kuce da dama shafukan sada zumunta inda wasu ke ganin ba girman jarumar bane ace ta rikice saboda ganin wani fitaccen jarumin dake sama da ita, yayinda wasu kume ke ganin cewa da gaskiyarta domin kuwa ganin jarumin dan kwallo irin Pogba abin alfahari ne a wurinta.

Haka kuma hotunan jarumar nata zagayawa a shafukan sadarwa na internet a yayin aikin Umarar nata wanda ya sanya aketa tafka muhawara kan wai shin jarumar Umara taje yine ko daukar hotuna?

 

Allah ya karbi ibadu amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *