A ranar 10 ga watan Mayun da muke cikine Dan Galadiman Kano Hakimin karamar hukumar Bebeji Alhaji Haruna Rasheed Sanusi ya rubuta takardar ajiye aikinsa zuwa ga ofishin babban sakataren gwamnatin jihar.

Masarautar Kano dai tana daga cikin manyan masarautu masu dinbin tarihi a Africa, a wannan karon ne dai gwamnatin jihar Kano ta rarraba masarautar zuwa sarakunan yanka biyar maimakon daya da take dashi a baya.

Dan Galadiman Kanon ya bayyana cewa ya ajiye mukaminsa ne saboda dalilai na lafiya, da kuma yanayin zamani da aka tsinci kai, a karshe yayi addu’ar neman zaman lafiya ga Kano da kuma kasa baki daya.

Allah ya kyauta.

Kalli takardar da ya rubuta a kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *