Shahararren Dan wasan kwallo kafa da yayi fice a Duniya Christiano Ronaldo Wanda yake bugawa Kungiyar Kwallon kafa ta Juventus dake kasar Italiya ya shawarci Shugabannin kulob din nasa akan cewa yana so su bude bakin aljihu domin su kawo mai wasu ‘yan wasa guda 6 da zasu taya shi murza Leda a Kulob din nashi.

Yan wasan dai da Ronaldo dai yake son Kungiyar shi ta Juventus ta kawo masa sun Hadar da Joao Felix Wanda yake taka Leda a kungiyar Kwallon kafa ta Benfica Dan Asalin kasar Portugal.

Baya ga haka Ronaldo yana so a siyo masa Isco da Raphael Varane, tsoffin Yan wasan da ya taka Leda tare dasu a tsohuwar Kungiyar shi ta Real Madrid, yayin da ya bayyana tsoffin abokan wasan nasa a matsayin wadanda zasu bayar da gudummowa sosai tare da Karfafar Kungiyar tashi ta Juventus.

Ragowar ‘yan wasan dai sune Federico Chiesa Wanda ke bugawa Kungiyar Fiorentina da Italiya; akwai Dan wasan Lyon Tanguy Ndombele; da kuma Matthijs de Ligt Wanda ke bugawa Kungiyar Kwallon kafa ta Ajax da Kostas Manolas Dan wasan Roma Dan Asalin kasar Greece.

Jaridar Correire dello Sport ta bayyana cewa wannan Shawarar dai Ronaldo ya tattauna ta da Kochin Kungiyar Max Allegri.

Ronaldo shine dan wasa daya tilo da ya dauki kofuna daga Mabanbanta kulob-kulob dake kasashen Portugal, England, Spain da kuma Italy.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *