Ministan aikin noma da raya karkara Audu Ogbeh ya bayyana farin cikinsa kan yadda Najeriya ke noma kashi 90 cikin 100 na shinkafar da ake ci kulli yaumin a kasar, ya fadi hakan nan ranar Talata a taron bincike da shirye-shirye da aka gudanar a kwalejin ilimin binciken aikin noma dake Zariya, jihar Kaduna.

Taken wannan taro shi ne inganta fitar da amfanin gona kasashen waje a Najeriya rawar ganin da masu ruwa da tsaki zasu taka.

Ogbeh wanda ya samu wakilcin Karima Babangida daraktar fitar da amfanin gonan ma’aikatar, ta bayyana yadda gwamnatin shugaban Buhari ke mayar da hankali kan yadda ‘yan Najeriya zasu rika noma abincinsu da kansu sabanin shigo da su daga kasashen ketare.

Jawabinsa ya ce misali daya da zan baku shi ne a yanzu aka mun shaida shine noman shinkafa, Najeriya ta kasance kasa mafi shigo da shinkafa daga kasar Thailand a duniya, amma a yau, mun samu canji wanda ya kai kashi 90 cikin 100 na shinkafan da muke ci a Najeriya a kasar nan ake nomashi, ya kamata mu yabawa manomanmu.

Najeriya na da ikon ciyar da kanta, kana ta zama babba a fitar da amfanin gona wasu kasashen nahiyar Afrika, Turai, Amurka da Asiya , musamman kasar Sin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *