Ficeccen jarimin fina-finan Hausa na masana’antar Kanywood Adam A. Zango zai angonce karo na shida a ranar juma’a mai zuwa da misalin karfe 2:30pm na rana a fadar mai martaba sarkin Gwandu dake jihar Kebbi

Adam A. zango dai zai yi aure 6 wanda tun shekara ta 2006 kawo yanzu, kuma matarsa ta farko ita ce Amina da ya Aure a 2006 ta haifi Yaro mai suna Haidar wanda yanzu shekarasa 12, sai Amaryarsa ta biyu ita ce Aisha ‘yar shika dake cikin Garin Zariya a jihar Kaduna wanda ta haifi ‘ya’ya uku 3 Maza, sannan akwai kuma Matarsa ta uku 3 Mai suna Maryam ‘yar jihar Nasarawa, haka zalika ya sake aure na 4 A Lugbe cikin Birnin Yola jihar Adamawa inda ya Auri Maryam AB,

Wanda a cikin shekara ta 2015 Adam A. Zango ya karayin Aure a sirrince inda ya auri wata mata mai suna Ummikulsum mai shekaru 34 A Garin Ngaoundere cikin kasar Kamaru kuma ta haifi yarinya d’aya mai suna Murjanatu

Inda yanzuanzu haka Adam A. Zango zai sake angwancewa da Amaryarsa Safiyya Umar Chalawa wacce akafi sani da (Suffy) a ranar juma’a mai zuwa, kuma bayanai dai sun tabbatar da cewar yanzu haka Adam A. Zango bashi da Mata ko d’aya sakamakon sakinsu da ya yi baki dayan su.

Menene ra’ayin ku kan irin wannan Auren da Adam A. Zango ke yi?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *