WATA RANA…………….!!!!

Magidanci ne yana da matan sa 3 da kuma ‘ya’ya 14, yana zaune ne a birnin Jos dake jihar Plateau.

Duk kuwa da Auren sa da kuma tarin ‘ya’ya,bai daina neman tsohuwar Budurwar sa ba, wacce suke haduwa a wani gidan sa suna sabon Allah, koda yake itama tana da Auren ta.

Ran nan kawai sai tsohuwar budurwar tasa,

kuma matar Aure ta nemi mijin ta ya barta taje garin su dake wani qauye a Bauchi,domin halartar bikin wata cikin dangin su.

Fitar ta ke da wuya bayan amincewar mijin, sai kawai ta zarce gidan tsohon saurayin ta,kuma mijin wasu matan.

Bayan sun gama lalata da lalacewa a dakin tsohon saurayin, sai kuma rashin lafiya ta rufe ta,a qarshe dai tace ga garin ku nan,ta bar duniya ta koma ga mahaliccin ta.

Ganin hakan ta faru,sai tsohon saurayin ya firgice kuma hankalin sa ya tashi,ya dauke gawar ta yaje wani waje ya jefar da ita.

Da aka kwana 2 mijin ta bai ganta ba,sai ya kirawo iyayen ta dake Bauchi domin tambayar me ya faru,kuma ya taya su murnar bikin ‘yar uwar matar sa.

Sanar dashi cewa ba wani biki fa da ake,kuma babu wanda ya ganta a Bauchi,sai wajen ‘yan Sanda ana cigiyar ta.

A cikin wasu ‘yan uwan ta maza,suka yi tunanin dama tana kai ziyarar asiri ga tsohon saurayin ta duk kuwa da kasancewar tayi Aure.

‘Yan sanda kuwa suka cafko shi,suka kuma fara yi masa tsauraran tambayoyi da dan ta6a lafiyar sa,har dai ya bayyana abinda ya faru,suka je ya nuna musu inda ya jefar da gawar.

Yanzu dai tsohon saurayi kuma magidanci yana hannun jami’an tsaro,da zarar sun gama bincike zasu miqa shi gaban Alqali.

Allah ya kare mu daga cin amana da sabawa dokokin Allah a boye ne ko a fili!!

Allah ya kare mana mutuncin mu dana iyalan mu baki daya!!!!!

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *