[Kiwon Lafiya] Marasa lafiya na rasa rayukansu sanadiyar turasu Asbitoci masu zaman kansu da Likitoci keyi a Lagos

 

Gwamnatin jihar Lagos ta kaddamar da bincike na musamman akan wasu Likitoci dake aiki a wasu daga manyan asibitocin jihar, bisa zargin jefa rayuwar marasa lafiya cikin hatsari ta hanyar turasu zuwa asibitocinsu masu zaman kansa domin cigaba da lura da lafiyarsu.

 

Kwamishinan Lafiya na jihar Lagos Dr Jide Idris, shine ya bayyanawa manema labarai hakan inda yace yin binciken ya zama dole saboda sun samu korafe-korafe da dama akan wannan batu.

 

Kamfanin dillanci labarai na kasa NAN ya rawaito cewa a cikin wannan watan na Maris da muke bankwana dashi an samu irin wannan matsalar inda wani likita asibitin Alimosho General Hospital ya tura wani karamin yaro dan wata 15 zuwa asibitinsa mai zaman kansa inda ya rasa ransa a can a wannan makon da muke ciki.

 

Allah ya kyauta.

 

Rahoto: Basheer Sharfadin Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *